The Biggest Technology Blogging Platform 2019.
Create 1 Suitable Post Earn 50

Featured Post

AMFANIN MAAN ZAITUN WAJEN GYARAN GASHI

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku bayanin yadda ...

  • AMFANIN MAAN ZAITUN WAJEN GYARAN GASHI
    Posted by

    AMFANIN MAAN ZAITUN WAJEN GYARAN GASHI
  • Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku bayanin yadda za ku yi amfani da man zaitun wajen gyaran gashi. Man zaitun na da matukar muhimmanci a jikinmu. Ana amfani da shi a matsayin man kitso.
    ==> Da farko a samu man zaitun mai kyau, sai a sanya shi a murhun zamani da ake kira ‘microwabe’ ko a sanya a cikin tukunya, sai a dora shi a murhu, sannan a bar shi ya yi dumi kamar tsawon minti 10.
    ==> Daga nan a rika amfani da hannu wajen dibar man zaitun din ana shafa wa shi a karkashin gashin kai. Haka za a rika shafawa har sai gashin ya gaurayu da man gaba daya.
    ==> A tabbata gashin a tsefe yake, sai a rufe shi da hular leda kamar na tsawon minti talatin. Bayan minti talatin, sai a wanke kan da man ‘shampoo’ da na ‘conditioner’.
    Idan aka ci gaba da wanke gashin kai za a samu canji, domin gashin zaizama mai sheki da santsi da laushi da kuma tsayi.

    No comments:

    Post a Comment