The Biggest Technology Blogging Platform 2019.
Create 1 Suitable Post Earn 50

Featured Post

AMFANIN MAAN ZAITUN WAJEN GYARAN GASHI

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku bayanin yadda ...

  • GYARAN GASHI
    Posted by

    GYARAN GASHI
  • Gashi kamar sauran bangarori na jikin dan Adam shi ma yana bukatar kulawa kwarai da gaske. Idan ya kasance gashi ba ya smaun kulawar da ta kamata to babu shakka zai kararraye ya kuma kade saboda iska ko rashin cikkakkiyar kula. Ga wasu hanyoyi da ya kamata mace ta bi wajen kula da gashinta.
    ==> Idan za a wanke gashi a yi mishi abin da ake kira steaming. Wata hanya ce ta wanke gashi bayan an shafe gashin da hadin manshanu ko kuma na kanti sai a sami hular leda ko kuma ledar a rufe gashin da ita. Bayan ya dauki kamar mintuna 30 sai a sa sabulu a wanke gashin tas da ruwan zafi da kuma sabulun wankin gashi mai kyau.
    ==> Ya kasance da zarar gashin ya bushe a shafe shi da mai sosai. Ma’ana abi gashin layilayi a rika shafa masa mai (Abin da ake kira da turanci oiling).
    ==> Akwai bukatar a rika kitso akaiakai saboda yawan tazar gashin shi ma hanya ce da ke sanya gashi kadewa.
    ==> A rika shafawa kitson mai (wanda ake amfani da shi don gashi) a kullum saboda ana bukatar kullum gashin ya kasance cikin danshi kada ya ya zama a bushe.
    ==> A kula cewa a lokacin hunturu man gashi mai ruwa wanda ake kira oil shi ya fi kyau ga gashi.
    ==> A rage yawan sanya wa gashi man shamfo (relader). A rika bari yana daukar tsawon watanni kafin akai ga yin shamfo. Idan ya kasance gashinki mai tauri ne ki yawaita yin sitimin a maimakon shampoo.

    No comments:

    Post a Comment