The Biggest Technology Blogging Platform 2019.
Create 1 Suitable Post Earn 50

Featured Post

AMFANIN MAAN ZAITUN WAJEN GYARAN GASHI

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku bayanin yadda ...

  • Cin Kayan Lambu Na Bayar Da Kariya Daga Cutar ‘Endometriosis’ Mai Hana Haihuwa
    Posted by

    Cin Kayan Lambu Na Bayar Da Kariya Daga Cutar ‘Endometriosis’ Mai Hana Haihuwa
  • Wani likita a fannin cututtukan mata a Nijeriya dakta Adewole Akintoyose ya yi kira ga mata da su jimirci cin kayayyakin itatuwa da na lambu domin kare kansu daga wata cuta mai hana haihuwa mai suna “endometriosis” a turance.
    Adewole, wanda ma’aikaci ne a asibitin St Leo da ke unguwar Lekki a jahar Lagos ya ce wannan cuta ta fi yawaita a tsakanin mata ‘yan shekaru 25 zuwa 40.
    A fadarsa, Cutar na yin lahani ne ga mahaifa da kuma kwayayen da ke jikin mace. Likitan ya ce alamomin cuta sun hada yawan ciwon mara, zafi a yayin saduwa, yawan gajiya, zafi yayin fitsari, da sauran su.
    Sauran alamomin sun hada da rashin haihuwa da wuri, fara gani jinin haila da wuri, da daina haihuwa a lokacin da ya kamata.
    Ya gargadi mata da su rage cin naman shanu, wanda ya ce ka iya haifar da cutar, ya kuma shawarci su da su kara yawan kayan itatuwa da na lambun da suke ci, wanda hakan na matukar taimakawa wajen rage yiwuwar kamuwa da cutar.

    No comments:

    Post a Comment