The Biggest Technology Blogging Platform 2019.
Create 1 Suitable Post Earn 50

Featured Post

AMFANIN MAAN ZAITUN WAJEN GYARAN GASHI

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku bayanin yadda ...

  • KARIN NI'IMA
    Posted by

    KARIN NI'IMA
  • HADIN KAZA
    Wannan wani hadine na mussaman wanda zai karawa mace ni’ima kuma zai zauna acikin jikinta har tsawon wata uku zuwa shida batare datayi amfani da kayan da’a ba ko na bature.
    Kaza wadda bata fara kwai ba ridi nonon rakuma, zaki yanka ki zare hanjin ba tare da anyi mata dunduwa-gunduwa ba, sai a zare hanjinta cikin zumbutunta zaki gyara ridi ki shanya ya bushe, sai ki daka shi. Kina iya fara tafasa kazar, sannan ki zuba ridinki cikin zumbutun kazar sai ki zuba nonon rakuma ki daure zunbutun ki hada kayan miya kadan sai ki zubo nonon rakumar a ciki, ki ci gaba da dafawa har sai ya dahu sannan kici.
    HADIN KAZA KASHA NA BIYU
    Anso ayima budurwa ko amarya da bata rage saura sati day aba a daura mata aure domin yana kara gigita angonta. Anso lokacin da aka sanyawa budurwa ranar aure, idan ya rage saura wata daya ayi bikin, a hada mata kaza da nonon rakumi, bayan taci wannan sai a rinka bata gyada da kwakwa da aya ta ringa ci, wannan hadin kuma ana so a yishi ranar daren da zngo zai shigo daki dadaddare:
    Kankana
    Tuffa (apple)
    Ayaba manya guda uku
    Zuma
    Madara ta ruwa
    WANI HADI DABAN
    Na motso sha’awa
    1- Garin alkama
    2- Garin sha’ir
    3- Garin farar shinkafa
    4- Garin nikaken dabino
    5- Nonon akuya
    Wannan kaya ana hadasu tare da nonon akuya suyi kwana uku sai a dafa a hada su da nonon akuya a dinga sha. Wannan hadin ne na larabawan kasar yernan wanda suke kira da suna (ahmubasshara)
    Gargadi: idan mace ko namiji sun san basa kusa da juna kar su sha.

    No comments:

    Post a Comment